Guterres Ya Soki Wasu Kasashe Kan Kin Jinin 'Yan Gudun Hijra
Saktare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan matakin da wasu kasashe suka dauka na kin karbar bakin haure.
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto António Guterres babban saktare janar na Majalisar Dinkin Duniya yayin da ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka a kasar Habasha na ishara kan yadda wasu kasashen Turai suka rufewa 'yan gudun hijra iyakokinsu, yana mai cewa kasashen Afirka duk da irin matsin lambar tattalin arziki da suke fuskanta da kuma matsalolin tsaro da zamantakewa , amma iyakokin kasashensu a buke yake ga 'yan gudun hijra.
Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya ce matakin da wasu kasashen Turai suka dauka na rufe iyakokin kasashensu ga 'yan gudun hijra da bakin haure, abin bakinciki da takaici ne.
A ci gaba da jawabinsa António Guterres ya ce batutuwa kamar tabbatar da sulhu da tsaro, bunkasa tattali arziki yankin na daga cikin mahiman batutuwan da suke gaban shugabanin kungiyar tarayyar Afirka.
A ranar Lahadin da ta gabata ce, aka bude taron kungiyar kasashen Afirka wato AU karo na 32, da nufin tattaunawa maudu'ai da dama ciki kuwa harda batun 'yan gudun hijra a Adis Ababa babban birnin kasar Ethiopia.