An Fara Sauraron Shari'ar Shuwagabannin Boren Catalonia A Espania
Wato kotu a kasar Espania ta fara sauraron shari'ar shuwagabannin wadanda suke son ballewar yankin Cathalonia daga kasar Espania.
Kamfanin dillancin laraban IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa tuhumar da akewa shuwagabannin masu son bellewar sun hada da, tada hankali, bore, amfani da kudaden kasa ba ta hanyar da ta dace ba da kuma rashin biyayya.
Tun farko dai mai gabatar da kara wadannan mutane a gaban kotun ya bukaci a yanke masu hukuncin dauri kama daga shekaru 7 - 25 kan aikata wadannan laifuffuka. Amma Lauwan gwamnatin Espania ya bukaci Kotun ta yanke masu hukuncin dauri daga shekaru 7-12 a gidan kaso.
A ranar 01-Octoban-2017 ne wadannan mutane suka jagoranci zaben raba gardama don neman jin ra'ayin mutanen yankin Cathalonia na ci gada da kasancewa bangare na kasar Espania ko kuma ballewa daga kasar, wannan duk tare da gargadin da gwamnatin tsakiyar kasar ta yi masu na kada su yi hakan.
Sakamakon zaben raba gardamar dai ta nuna cewa mutanen yankin Cathalonia ba sa son ci gaba da kasancewa bangare na kasar Espania, amma babban kotun kasar ta bayyana sakamakon a matsayin wanda bai da inganci kuma ba ibin amincwa bane.
A lokacinda rikicin ballewar ya yi zafi dai shugaban masu son bellewar Carles Puigdemont ya arce daga kasar.