Trump Ya Bada Umurnin Kafa Rundunar Sojojin Amurka A Sararin Samaniya
A jiya Talata ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu a kan wata bukata ta samar da rundunar sojojin Amurka a sararin samaniya.
Kamfanin dillanin labaran Farsnews ya bayyana cewa wannan umurnin yana nufin rundunar sojojin sararin samaniya na kasar Amurka zata zama rashe na rundunonin sojojin kasar a karshin ma'aikatar tsaro ta Pentagon.
Bayan wannan umurnin dai hukumar ta Pentagon zata tsaro yadda rundunar zata kasance tare da hukumomin sararin samaniya na kasar wato NASA sannan ta gabatar da shirinwa majalisar dokokin kasar don jin ra'ayinta ko kuma don amincewa da shirin.
Da wannan kuma Amurka ta bawa kanta damar kai makamai zuwa sararin samaniya wanda zai bata damar kai hari a kan ko wace kasa a duniya daga sama.
Tunis dai wannan batun ya fusata kasashen duniya da dama, wadanda suka bayyana rashin amincewarsu da wannan shirin na Amurak, wannan ya sabawa dokokin kasa da kasa da dama daga cikin kasashen da suka nuna rashin amincewarsu a kwai kasar Iran.