Pakistan Ta Bukaci MDD Ta Shiga Tsakaninta Da Kasar India
Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasar Pakistan ta bukaci babban sakataren MDD Antonio Gutteres ya shiga tsakaninta da kasar India.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin babban sakatarin Stephane Dujarric yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa rikici yana kara tsanani tsakanin kasashen biyu a cikin yan kwanakin da suka gabata, don haka ne Islamabad ta bukaci tallafin babban sakatarin don rage rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.
Kafin haka dai a ranar Litinin da ta gabata ce kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasar ta bukaci jakadan Pakistan da ke New Delhi ya dawo gida don shawara, sanadiyyar zargin da gwamnatin India take wa gwamnatin Pakistan na cewa tana da hannun a wani harin da aka kaiwa sojojinta a yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar ta Pakistan.
A ranar Alhamis da ta gabata ce wani bom wanda aka dana a gefen titi ya tashi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar India 44 a garin Pulwama a yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar India. Gwamnatin kasar Pakistan dai ta musanta cewa tana da hannu cikin wannan harin.