Venezuela : Maduro Ya Rufe Iyakar Kasarsa Da Brazil
(last modified Fri, 22 Feb 2019 04:14:18 GMT )
Feb 22, 2019 04:14 UTC
  • Venezuela : Maduro Ya Rufe Iyakar Kasarsa Da Brazil

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela, ya bada umarnin rufe iyakar kasarsa ta hanyar kasa da Brazil, da kuma yin barazanar rufe ta Columbia.

Shugaba Maduro, wanda ke sanar da wannan matakin a wata ganawa da babban hafsan sojin kasar, ya bayyana cewa daga karfe 8:00 na dare agogon wurin, karfe 12:00 na daren ranar alhamis agogon GMT, iyakar kasar da Brazil zata kasance a rufe har zuwa wani lokaci.

Mista Mduro ya kuma yi barazanar rufe iyakar kasar da Columbia, wadda ya zargi shugaba, Ivan Duque, na Columbia da tsokana da kuma hadin kai da shugaban Amurka Donald Trump.

Matakin na Shugaba Maduro na zuwa ne a daidai lokacin aa inda jagoran 'yan adawa na kasar wanda ya ayyana kansa shugaba, Juan Guado, ke shirin zuwa iyakar kasar da Clumbia domin shigo da tallafin jin kai na Amurka.

Wasu rahotanni na daban na cewa tuni wani ayarin motoci na M. Guado, wadan kasashen duniya 50 suka amince dashi a matsayin shugaban kasar na riko, da magoya bayansa suka bar Caracas babban birnin kasar zuwa yankin Tachira  dake yammacin kasar a iyaka da Columbia, da nufin shigo da tallafin.

A nasa bangare shugaban Maduro wanda ke ci gaba da samun goyan bayan kasashen Rasha da China na ci gaba da musanta cewa kasarsa na cikin mayuyalin halin da take bukatar tallafin gaggawa.