Gwamnatin Kasar China Na Ci Gaba Da Takura Musulmi
Gwamnatin kasar china ta lakafa kamarori a yankin da muuslmi suke da zama domin sanya ido a kansu da kuma harkokinsu.
shafin yada labarai na Magrib yaum ya bayar da rahoton cewa, a ci gaba da daukar matakan takurawa kan musulmi, gwamnatin kasar china ta lakafa kamarori a yankin Sing Kiyang na musulmi domin sanya ido a kansu da kuma dukkanin zirga-zirgarsu da sauran harkokinsu na yau da kullum.
Rahoton ya ce wadannan kamarori suna sanya ido a kn musulmi sama da miliyan biyu da rabi da ke yankin, wadanda suke fuskantar gallazawa daga jami’an tsaron gwamnatin kasar ta China.
Yanzu haka akwai miliyoyon muusulmi da China ta tsare a wani sansani tare da hana su gudanar da harkokinsu, inda ake tilasta su cin naman alade da kuma shan giya, kamar yadda a cikin watan azumi ake tilasta su cin abinci da rana.