Venezuela: Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Shugaba Maduro
Dubun-dubatar jama'a a birnin Caracas na kasar Venezuela suna ci gaba da gudanar da gangami a kan titunan birnin domin nuna goyon baya ga shugaban kasar Nicolas Maduro.
Wannan yana zuwa ne a lokacin da ake sa ran a yau ne kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai kada kuri'a kan wasu kudurori guda biyu da Amurka ta gabatar da kuma wanda Rasha ta gabatar a ga kwamtin kan batun Venezuela, wadanda dukkaninsu sun yi karo da juna.
Kasar Amurka dai tana hankoron ganin ta kawo karshen salon mulkin da kasar Venezuela take tafiya a kansa, wanda tsohon shugaba kasar marigayi Hugo Chavez ya dora kasar a kai, na kin mika wuya ga manufofin siyasar Amurka, a yayin da Amurka take son hambarar da gwamnatin kasar domin dora wadanda za su yi mata biyayya sau da kafa.
Baya ga goyon bayan mafi yawan al'ummar kasar da shugaba Maduro yake samu, dukkanin rundunonin sojin kasar da sauran bangarori na tsaro sun jaddada goyon bayansu gare shi, tare da shan alwashin fuskantar duk wata barazana ta Amurka a kan kasarsu har zuwa bayan ransu.