Faransa: Ana Ci Gaba da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati
(last modified Sun, 03 Mar 2019 07:36:43 GMT )
Mar 03, 2019 07:36 UTC
  • Faransa: Ana Ci Gaba da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati

Masu Zanga-zangar da su ka shahara da sanya tufafi mai launin ruwan dorawa, sun  shiga mako na goma sha shida a jere a jiya Asabar.

Manufar Zanga-zangar wacce ta fara tun a karshen shekarar 2018 da ta shude, shi ne nuna adawa da siyasar tattalin arziki ta shugaba Macron, wacce ta kunshi kara farashin makamashi.

A birnin Paris masu Zanga-zangar sun yi cinirindo a bakin ginin ma’aikatar tattalin arziki da kuma ta harkokin waje. An girke jami’an tsaro a sassa daban-daban na birnin Paris domin hana barnata dukiyar al’umma.

Masu Zanga-zangar sun fusata da furucin da shugaban kasar Emannuel Macron ya yi, na dangantasu da mabarnata. An kuma gudanar da Zanga-zangar a cikin wasu biranen kasar ta Faransa.

A tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da Zanga-zangar jami’an tsaro sun kashe mutane 10 tare da jikkata wasu 3,300.