Amurka Ta Tsawaita Takunkumin Da Ta kakabawa Zimbabwe
A jiya Litinin ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu akan tsawaita takunkumin kasar kasar Zimbabwe saboda abin da ya kira ci gaba da yi wa manufofin Amurka barazana da take yi.
Amurkan ta kara tsawaita takunkumin ne duk da kiraye-kirayen da kasashen nahiyar Afirka da su ka hada da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, na ganin an dage wa Zimbabwe takunkumin domin tattalin arzikinta ya farfado.
Gwamnatin Donald Trump ta bayyana cewa takunkumin zai cigaba har zuwa lokacin da gwmanatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta sauya dokokin da suke takurawa kafafen watsa labaru, ‘yanci da kuma kyale mutane su yi Zanga-zanga.
Majiyar Amurka ta ce takunkumin nata ya shafi ma’aikatu, cibiyoyi da kuma daidaikun mutane da su ka kai 141, daga cikinsu hadda shugaba Mnangagwa da tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.