An Shiga Kwana Na Uku Babu Wutar Lantarki A Venezuela
A yau Lahadi an shiga kwana na uku a jere ba tare da wutar lantarki ba a kasar Venezuela, bayan wani farmakin da aka kaiwa tsarin wutar lantarkin kasar ta hanyar yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da fuskantar karin matsaloli a kasar Venezuela bayan daukewar wutar lantarki babu zato babu tsammani tun daga daren Juma'a da ta gabata.
Shugaban kasar ta Venezuela da ke takon saka da Amurka Nicolas Maduro ya bayyana cewa, bayan yakin da makiya suke yi da kasar ta bangarorin siyasa da tattalin arziki har ma da yi wa kasar barazana ta tsaro, yanzu kuma sun kaddamar da yakin wutar lantarki a kasar ta Venezuela da nufin ci gaba da kara dagula lamurra a kasar.
Maduro ya ce kamar yadda suka yi tsayin daka wajen kin mika wuya ga matsin lamba na mul;kin mallakar Amurka da masu yi mata amshin shata, haka ma za su yi tsayin daka wajen fuskantar wannan makirci na hankoron haramtawa al'ummar Venezuela wutar lantarki.
Ministan wutar lantarki na kasar ta Venezuela ya bayyana cewa, an kai hari ne na yanar gizoa cikin tsarin wutar lantarkin kasar, inda aka kutsa cikin tsarin ta hanyar yanar gizo aka bata shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar daukewar wuta akasar baki daya, kuma duka maganar ta siyasa ce, domin manufar hakan dai a fili take, kuma wadanda suka yi hakan a fili suke, domin kuwa in banda Amurka babu wata kasa da za ta iya yin wannan kutsen, kuma manufar ita ce domin a tunzura al'ummar kasar su ki gwamnatin shugabab Maduro.