Amurka: Alkalumma Sun Nuna Cewa Musulmi Su Ne Suka Fuskantar Tsangwama
Wani sakamakon jin ra’ayin jama’a a kasar Amurka ya nuna cewa musulmi su ne suka fi fuskantar tsangwama a kasar.
Jaridar Yani Shafaq ta bayar da rahoton cewa, wasu manyan cibiyoyin bincike a kasar Amurka sun gudanar da jin ra’ayin jama’a, wanda sakamakonsa ya nuna cewa musulmi su ne suka fi fuskantar tsangwama a kasar da kuma nuna musu wariya.
Bayanin ya ci gaba da cewa, cibiyoyin Harrisx da Hill ne suka gudanar da binciken an hadin gwiwa a dukkanin jahohin Amurka.
Kimanin kashi 85 cikin dari na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun nuna cewa musulmi ne suka fi fuskantar matsala da kuma nuna musu wariya saboda addininsu a kasar.
Da dama daga cikin cibiyoyin musulmi a kasar Amurka sun bayyana cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, an samu matsaloli na cutar da musulmi fiye da sauran shekarun da suka gabata a kasar.