Turai Ta Rufe Sararin Samaniyarta ga jiragen Boeing 737 MAX
Kasashen turai sun sanar da rufe sararin samaniyarsu ga jiragen sama kirar kamfanin Boeing na Amurka, samfanin 737 Max.
Hakan dai na zuwa ne bayan hatsarin jirgin kamfanin Ethiopien airlines a ranar Lahadi data gabata wanda yayi ajalin mutum 157, kuma a kasa da watanni shida bayan irin hakan ta faru ga wani jirgin irin samfarin na 737 Max.
Kasashen da suka dakatar da zurga zurka ta jiragen sun hada da Faransa, jamus, Ingila, Hollande, Italiya.
Dama dai kafin hakan kasashen Asiya da kuma na yankin golfe da dama sun jingine aiki da jiragen samfarin Boeng 737 Max
A Amurka kuwa fasinjoji ne suka ki hawan jiragen Boeing 737 MAX, duk da tabatancin da kamfanin da Boeing, yabayar kan ingancin jiragen.
Wannan dai shi ne kusan karon farko da irin hakan ta faru ga harkokin surufin jiragen sama a duniya.