Faransa: Adadin Mutane Marassa Wurin Kwana Ya Kai 566
Wasu alkalumma da cibiyoyin da suke da dangantaka da gwamnatin kasar Faransa suka fitar sun nuna cewa, adadin wadanda ba su da wurin kwana a kasar ya kai 566 a cikin shekara ta 2018 da ta gabata.
Bayanin ya ce matsakaitan shekarun mutanen yana kamawa ne tsakanin shekaru 48 zuwa sama ko kasa, wasu daga cikin su kuma mata ne.
Haka nan kuma akwai kanan yara 13 wasu daga cikinsu ‘yan kasa da shekaru 5 ne.
Wannan dai na faruwa ne sakamakon matsaloli na rashin aikin yi da irin wadannan mutane suke fama da su a kasar ta Faransa.
Haka nan kuma wasu cibiyoyi masu zaman kansu sun bayyana cewa, adadin mutane da suke fama da matsaloli na rashin wurin kwana a kasar ta Faransa, ya ninka wannan adadi da aka bayar.