Mar 20, 2019 05:25 UTC
  • MDD Ta Bukaci Isra'ila Ta Gudanar Da Sauyi A Dokokin Sojinta

A yayin da aka kwashe shekara guda ana gudanar da zanga-zangar neman dawo da hakkin kasa a yankin Palastinu, Hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta ce akwai bukatar Isra'ila ta gudanar da sauye-sauye a jerin dokokin jami'an tsaronta.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto kwararu na hukumar kare hakin bil-adama ta MDD na cewa bayan binciken da suka gudanar a game da zanga-zangar neman dawo da hakki da al'ummar Palastinu suka fara tun a shekarar 2018 din da ta gabata, sun fahimci cewa a jerin dokokin bangaren tsaron Isra'ila, jami'in tsaro nada hakin bindige duk wani da ya halarci zanga-zanga, wanda kuma hakan ya sabawa dokokin kare hakin bil-adama na kasa da kasa, don kuwa akwai bukatar Isra'ila ta canza wannan doka.

Jami'in ya ce duk da cewa a cikin dokar,  jami'in tsaron Isra'ilan nada hakin harbin wanda ya halarci zanga-zangar a kafarsa ne, to amma abinda jami'an tsaron Isra'ila suke aiwatarwa ya sabawa wannan doka, don haka muke bukatar hukumomin Isra'ilan, kwata-kwata sun soke  wannan doka.

Ko baya ga hakan, jami'in ya tabbatar da cewa abinda jami'an tsaron Isra'ilan ke aikatawa, ya sabawa dokar kare hakin bil-adama  na kasa da kasa .