Ministocin Harkokin Waje G7, Sun Halarci Taron Adu'o'i Hiroshima
https://parstoday.ir/ha/news/world-i3733-ministocin_harkokin_waje_g7_sun_halarci_taron_adu'o'i_hiroshima
Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki, ciki har da John Kerry, sun halarci taron tunawa da wadanda suka mutu a Hiroshima.
(last modified 2018-08-22T06:58:07+00:00 )
Apr 10, 2016 23:47 UTC
  • ministocin harkokin wajen kasashen G7 a adu\'o\'i Hiroshima (hoto @ TOSHIFUMI KITAMURA / AFP)
    ministocin harkokin wajen kasashen G7 a adu\'o\'i Hiroshima (hoto @ TOSHIFUMI KITAMURA / AFP)

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki, ciki har da John Kerry, sun halarci taron tunawa da wadanda suka mutu a Hiroshima.

Mr Kerry dai ya kasance wani babban jami'in Amurka da ya ziyarci Hiroshima tun bayan da Amurka ta jefa makamin kare dangi da ya yi ragargaza birnin a 1945.

Kafin hakan dai wani jami'in Amurka ya bayana a jiya Lahadi cewa, Mr Kery ba zai nemi gafara ba da sunan Amurka dangane da abunda ya faru a Hiroshima, aman Amurka dama al'umma Japon din na bakin cikin abunda ya faru.

Mr Kerry ya je birnin na Hiroshima ne domin halartar taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki, domin tattauna batutuwan da suka shafi ta'addanci da halin da ake ciki a yankin Gabas Ta Tsakiya da kuma matsalar 'yan gudun hijira.