Wata Daliba Musulma A Amurka Ta Bayyana Yadda Take Fuskantar Tsangwama
Wata daliba musulma a makarantar Hill da ke jahar Peselvania a Amurka ta bayyana yadda take fuskantar matsalar kyama daga wasu Amurkawa.
Shafin yada labarai na Reading Eagle ya habarta cewa, Su’ad Al-bahwati ta ce tun daga lokacin da ta fara saka cikakken hijabin muslunci take fuskantar matsaloli a rayuwarta ta zamantakewa.
Su’ad ta ce hakan baya rasa nasaba ne da abin da yake faruwa a duniya a halin yanzu na ta’addanci, inda wasu suke amfani da sunan addinin musulunci wajen aikata muggan laifuka na kisan bil adama da sunan jihadi.
Ta ce ko shakka babu wanan ya bar mummuna tasiri a cikin kwakwalen mutanen nahiyar turai dangane da addinin musulunci, inda da dama suke kallon musulmi a matsayin yan ta’adda.