Equador : Girgiza Kasa Ta Kashe Mutane 77
Apr 17, 2016 05:21 UTC
-
girgiza a yankin Manta na Equador
Hukumomi a Equador sun ce adadin mutanen da suka rasa su sakamakon a girgiza kasa data auku da yammacin jiyya Asabar ya kai 77, kana wasu 588 suka raunana.
Mataimakin shugaban kasar Jorge Glas ne ya sanar da hakan, a yayin da masana ke cewa karfin girgizan kasar ya kai maki 7.8
wannan dai ita ce girgiza kasa mafi muni da aka fuskanta a wannan kasa tun bayan shekara 1979.
Yanzu haka dai masu aikin cewa na ci gaba da agazawa mutanen da wannan iftila'in ya rusa dasu, a yayin da yanzu haka aka bayyana dokar ta baci a yankuna shida na kasar.