An Bukaci Gudanar Da Zaben Raba Gardama Kan Makomar Sarautar Ingila
Jam'iyyar Republican ta kasar Britania ta bukaci a gudanar da zaman raba gardama
Jam'iyyar Republican ta kasar Britania ta bukaci a gudanar da zaben raba gardama a kasar bayan mutuwar Saraunia Elizabath II. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto sakatarin gudanarwa na jam'iyyar Graham Smith yana fadar haka a jiya Alhamis a dai dai lokacinda ake bukukuwan cika shekara 90 da haihuwar Sarauniyar a birnin London.
Smith ya kara da cewa mafi yawan mutanen kasar Britania basa da ra'ayin ci gaba da tsarin sarauta a kasar, don haka akwai bukatar a gudanar da zaben raba gardama kan makamar tsarin sarauta na kasar, wanda babu abinda yake tunatarwa, sai irin zaluncin da tsarin ya aiwatar a duniya.
A halin yanzu dai Saraunia Elizabeth ta ciki shekaru 63 kan kujerar sarautar kasar Britania, sannan ita ce sarauniyar wasu kasashe 16 a duniya masu cin gashin kansu. Banda haka Saraunair Ingila ce shugabar kungiyar Commanwealth ta kasashe ranon ingila 54 a duniya.