MDD : Kwamitin Tsaro Zai Cirewa Ivory Coast Takunkumin Makamai
-
zauren kwamitin tsaro na mdd
A gobe Alhamis ake san ran kwamitin tsaro na MDD zai cirewa kasar Ivory Coast takunkumin sayan makamai na tsawan shekaru 12 da aka kakaba mata.
Kazalika kwamitin zai tsawaita aikin tawagar sa ta zamen lafiya da shekara guda ta karshe a kasar ta Ivory Coast, kamar yadda jakadan kasar Faransa, François Delattre ya sanar a zauren na majalisar dinkin duniya.
kasar Faransa ce dai ta gabatar da wannan kudirin a zauren na MDD dake neman a cirewa kasar ta Ivory Coast takunmin da aka kakaba mata tun cikin shekara 2004 bayan yakin basasa daya barke tsakanin magoya bayan tsaohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da kuma shugaba mai ci Alassane Ouattara, wanda ya kai ga Faransa ta dau matakin aikewa da sojojin ta a kasar domin kare al'umma da dukiyoyin su.
A hannu daya kuma kudirin ya nemi da a toshi kadarorin da kuma hana tafiye-tafiye ga wasu mayan jam'ian kasar ta Ivory Coast su shida ciki harda Laurent Gbagbo dake fuskantar shari'a yanzu haka gaban kotun hukunta mayan laifuka ta duniya wato ICC.