Ministan harkokin Wajen Biritaniya Ya Ziyarci Cuba
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4528-ministan_harkokin_wajen_biritaniya_ya_ziyarci_cuba
Ministan harkokin wajen kasar Biritaniya Philip Hammond, ya kai wata ziyara a kasar Cuba, wace ke zamen ta farko ta wani babban jami'in kasar ta Biritaniya tun bayan shekara 1959.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 01:22 UTC
  • ministan harkokin wajen Biritaniya, Philip Hammond
    ministan harkokin wajen Biritaniya, Philip Hammond

Ministan harkokin wajen kasar Biritaniya Philip Hammond, ya kai wata ziyara a kasar Cuba, wace ke zamen ta farko ta wani babban jami'in kasar ta Biritaniya tun bayan shekara 1959.

Wannan ziyara ta zo ne a cikin ran-gadin da ministan keyi a yankin kasashen Latin-Amurka.

Mr Hammoud ya bayyana a wani taron manema labarai cewa yana mai farin ciki da wannnan ziyara a birnin Havana tun bayan juyin juya halin shakara 1959.

A yayin ziyara Mr Hammond ya samu ganawa da takwaransa na Cuba, Bruno Rodriguez.

kazalika kasashen biyu sun cimma yerjejeniyo da dama a tsakaninsu da bunkasa alaka a fanonin da suka shafi kudi, makamashi, al'adu da ilimi mai zurfi.