Duniya Zata Taimakwa Libya Akan Yaki Da Kungiyoyin Jihada
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5296-duniya_zata_taimakwa_libya_akan_yaki_da_kungiyoyin_jihada
Mayan Kasashen duniya da kasashen makoftan Libya sun goyi bayan gwamnatin Libya akan mallakar makamai domin yaki da kungiyoyi jihadi
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 17, 2016 07:28 UTC
  • Duniya Zata Taimakwa Libya Akan Yaki Da Kungiyoyin Jihada

Mayan Kasashen duniya da kasashen makoftan Libya sun goyi bayan gwamnatin Libya akan mallakar makamai domin yaki da kungiyoyi jihadi

babban sakataren gwamnatin Amurka John Kerry ya bayyan a jiya a Vienna cewa, kasashen 25 da kungiyoyin kasa da kasa sun cimma matsaya guda ta ganin an dage kasar takunkumin sayan makamai da aka kakaba mata tun cikin shekara 2011, ta yadda zata tunkari matsalar kungiyoyin 'yan ta'ada irin su Da'esh da sauran su masu ikirarin jihadi.

a hannu daya kuma kasashen sun kore duk wata jita-jitan cewa suna shirin aikewa da dakarunsu a kasar ta Libya domin taimakawa gwamnatin hadaka ta Tripoli dake samun goyan mdd karkashin jagorancin Fayez al-Sarraj.