Muhammad Ali Ya Rasu
Jun 04, 2016 00:41 UTC
-
Dan wasan damben duniya, Mohammed Ali
Allah ya yiwa fitaccen zakaran damben daya kafa tarihi a duniya, Muhammad Ali rasuwa.
Muhammed Ali wanda aka kwantar dashi asibiti a jihar Arizona dake Amurka a wannan Alhamis, ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
An dai kwatar da shi asibiti saboda yana fama da cutar da ta shafi numfashi.
Muhammed Ali dai yayi ritaya daga dambe a shekarar 1980, amma a baya bayan nan yana fama da rashin lafiya.
Sunansa na ainihi dai shi ne Cassius Clay, amma ya koma Muhammad Ali bayan ya musulunta a shekarar 1964 lokacin da karon farko ya zama zakaran damben boxe na duniya.