An kashe wani Dan jarida na Amurka a Afganistan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6304-an_kashe_wani_dan_jarida_na_amurka_a_afganistan
Wata Radion Gwamnatin Amurka ta sanar da kisan Dan kasar marubicin jarida tare da mai yi masa tarjama a kudancin Afganistan.
(last modified 2018-08-22T06:58:23+00:00 )
Jun 06, 2016 01:06 UTC
  • An kashe wani Dan jarida na Amurka a Afganistan

Wata Radion Gwamnatin Amurka ta sanar da kisan Dan kasar marubicin jarida tare da mai yi masa tarjama a kudancin Afganistan.

Gidan Radion NFR na kasar Amurka ya sanar da cewa a jiya Lahadi Ma'aikacin gidan radion mai suna David Gilkey tare da mai yi masa tarjama Zabihul...Tamana a yayin da suke tafiya tare da Sojojin kasar Afganistan a garin Hilmand na kudancin kasar sun rasa rayukansu sandaniyar halbin su da aka yi.

Gidan Radion na NFR ya ce duk da cewa a yayin wannan aiki a kwai wasu 'yan jaridu biyu wato Tom Bowman da Monika Evstatieva dake tare da Gilkey, amma su harin bai ritsa da su ba.

Mista Michael Oreskes daya daga cikin shugabanin gidan Radion na NFR ya ce David Gilkey ya bayar da gudumursa sosai a yakin Iraki, Afganinstan da kuma harin 11 ga watan Satumba.

Mista David Gilkey ya samu lambobin yabo da dama kan irin jan kokarin da ya yi wajen hada rahotanni a kasashen Duniya, musaman a kasar Iraki da yankin Afirka.