A Juma'a Mai Zuwa Ne Za'a Yi Jana'izar Marigayi Muhammad Ali
Iyalan shahararren dan damben nan Muhammad Ali wanda ra rasu a Juma'ar da ta gabata sun sanar da cewa a ranar Juma'a mai zuwa ne za a gudanar da jana'izarsa da kuma bisne shi a garinsu na haihuwa wato Louisville, da ke jihar Kentucky a Amurka.
A wata sanarwa da iyalan marigayin suka fitar sun ce a ranar Juma'a mai zuwa ne, wato mako guda bayan rasuwarsa, za a gudanar da jana'izarsa suna masu cewa an jinkirta bisne shi ne din ne don ba da dama ga mutane da masoyansa daga sassa daban-daban na duniya halartar jana'izar.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci jana'izar har da tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton da wasu fitatttun 'yan wasan kwaikwayo da 'yan siyasa da 'yan jarida da sauransu. Har ila yau iyalan marigayin sun ce daga cikin wadanda aka gayyata din har da shugaban Amurkan Barack Obama sai dai har ya zuwa yanzu fadar White House ba ta bayyana ko shugaban zai sami damar halarta ba.
A yau ne dai aka kai gawar marigayi Muhammad Ali garin na su don ci gaba da shirye-shiryen jana'izar ta sa.
Tun bayan sanar da labarin rasuwar tasa, miliyoyin jama'a daga sassan duniya ke ta aikewa da sakonnin nuna juyayi da wannan rashi na zakaran zakarun damben na duniya wanda ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.