Obama Ya Taya Clinton Murna
Jun 08, 2016 06:46 UTC
Shugaba Barak Obama na Amurka ya taya uwal gida Hillary Cliton murna saboda kasancewa 'yar takarar fidda gwani ta jam'iyyar Demokuradiya.
Obama ya taya Mme Cliton murna ne a wata hira ta wayar tarho, a yayinda yake jinjinawa 'yan takara biyu Bernie Sanders da Hillary Clinton akan yadda suka gudanar da yakin neman zaben su.
Madam Hillary Clinton, 'yar takarar jam'iyyar Demokuradiya a zaben shugaban kasar Amurka, ta samu yawan kujeru dake ba ta damar kasancewa 'yar takarar jam'iyyarta a zaben shugaban kasar Amurka dake tafe.
Tags