Sudan: Kamun Babban Mai Fatauncin Mutane
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6472-sudan_kamun_babban_mai_fatauncin_mutane
An Kame Mai Fataucin 'Yan gudun hijira A Kasar Sudan
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 02:18 UTC
  • Sudan: Kamun Babban Mai Fatauncin Mutane

An Kame Mai Fataucin 'Yan gudun hijira A Kasar Sudan

Jaridar al-Yaum Sabi'i, da ake bugawa a kasar Masar ta ambato wani jami'in kasar Sudan yana cewa; Mutumin da aka kama din dan asalin kasar Erittera ne mai suna Murid Mudhany.

Mutumin wanda ake bai wa sunan; 'Janar' ana zarginsa da mutuwar mutane 359 a cikin ruwan kasar Italia a 2013.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Kungiyar da ta ke fada da aikata laifuka a Birtaniya da kuma cibiyar tattara bayanai da tsaro ta kasar Italiya, sun rika bin diggidin mutumin inda su ka yi nasarar gano mabuyarsa da suka sanar da gwamnatin Khartum.

Wasu tuhume-tuhumen da Mudhani ya ke fukanta sun hada da mummunar mu'amala da 'yan gudun hijira da jefa rayuwarsu cikin hatsari.