A Yau ne za a kamala Jana'izar Muhamad Ali
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6514-a_yau_ne_za_a_kamala_jana'izar_muhamad_ali
A yau ne Za a kamala Jana'izar Shahararen Dan Danban nan musulmi Dan Kasar Amurka Muhamad Ali.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 10, 2016 00:25 UTC
  • A Yau ne za a kamala Jana'izar Muhamad Ali

A yau ne Za a kamala Jana'izar Shahararen Dan Danban nan musulmi Dan Kasar Amurka Muhamad Ali.

Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana Sama da 'yan jaridu dubu biyu ne gami da masu ɗaukar hoto daga ƙasashen duniya suka halarci wannan jana'iza da aka fara tun a jiya Alhamis da kuma za a kamala a yau Jumma'a.Tare da halarta wasu daga cikin shugabanin ƙasashen Duniya ciki kuwa har'da na Turkiyya Recep Tayib Erdogan.

Rahoton ya ce Shugaba Barack Obama bai samu damar halarta jana'izarba saboda wani uzirin da ke gareshi sai dai ya tura wakilinsa.

Muhammad Ali ya rasu a ranar Jumma'a da ta gabata yana da shekaru 74,kuma tun daga shekara ta 1984 ya fara jinya cutar zanzzanar jiki watau Parkison

Masu ibada da magoya bayan Muhammad Ali sun halartar taron addu'o'in da ake yi gwarzon dan damben a birnin Louisville na jihar Kentucky, da ke Amurka.

Al'umar Musulman Amurka da ke halartar addu'o'in sun ce suna fatan taron zai zamo wata dama ga Amerikawa su kare fahimtar addinin Musulunci da kuma aikace-aikacensa.

A shekarar 1964, Ali ya karbi addinin Musulunci, sannan ya sauya sunansa daga Cassius Clay, wanda ya ce sunan sa ne "bauta".