An Gudanar Da Jana'izar Marigayi Muhammad Ali A Amurka
Dubun dubatan mutane ne suka halarci jana'izar da aka yi wa zakaran zakarun damben duniyan nan marigayi Muhammad Ali wanda aka gudanar a garin haihuwar na Louisville na jihar Kentucky, da ke Amurka.
Rahotanni daga birnin na Louisville sun bayyana cewar Imam Zaid Shakir, wanda ya jagoranci taron addu'ar da aka fara yi wa marigayi Muhammad Ali tun a jiya Alhamis shi ne ya jagoranci yi masa salla kafin a bisne shi.
A cikin wasiyyar da ya bari marigayi Muhammad Ali ya bayyana cewa yana so a kare masa akidarsa ta Musulunci da kuma yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kamar yadda kuma ya bukaci a sanar da mutane da kuma share musu fagen halartar jana'izar tasa don kuwa a cewarsa shi na jama'a ne.
Shugabanni da manyan 'yan siyasa da fitattun mutane daga bangarori daban-daban na duniya ne suka halarci jana'izar tasa ta yau, cikinsu kuwa har da shugaban kasar Turkey Rajab Tayyib Erdogan sai da kuma yayi saurin barin wajen jana'izar sakamakon abin da wasu suka fassara da fushin da yayi sakamakon hana shi jagorantar addu'oi da karatun Alkur'ani mai girma da aka yi a wajen.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce Muhammad Ali ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.