Faransa Ba Tada Niyyar Tura Sojojin Kasa A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i709-faransa_ba_tada_niyyar_tura_sojojin_kasa_a_siriya
batun tura sojojin kawance domin yaki a Siriya na ci gaba da raraba kanuwan kasashen duniya.
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 13, 2016 07:50 UTC
  • Firaministan Faransa Manuel Valls
    Firaministan Faransa Manuel Valls

batun tura sojojin kawance domin yaki a Siriya na ci gaba da raraba kanuwan kasashen duniya.

Kasar Faransa ta ce ba tada niyyar tura sojojin kasan ta a kasar Siriya ba kamar yadda firaministan kasar Manuel Valls ya sanar.

Valls ya kara da cewa kasashen da batun ya shafa na da zabi akan su tura sojojin su ko kuma A'a, aman kasar sa ba tada niyyar tura nata sojoji.

batun tura sojojin kawance domin yaki a kasar Siriya na daya daga cikin batutuwan da yanzu haka kasashen duniya ke ci gaba da kace-nace kan sa.

A nata bangare dai Kasar Sin ta bakin ministan harkokin wajen ta ce, ba zata shiga ko wane kawance ba na yaki da ta'adanci a gabas ta tsakiya, aman a shirye ta ke ta taimakawa kasar Irak.