Magajin Garin Birnin Chicago na Amurka Ya Gayyaci Taron Buda Baki
Magajin garin birnin Chicago na kasar Amurka ya gayyaci taron buda baki wanda ya hada musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.
Shafin yada labarai na Arab Daily News ya bayar da rahoton cewa, Ram Emanuel magajin garin birnin Chicago ya gayyaci taron buda bakin ne a jiya Talata, inda musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suka karba goron gayyatarsa suka halarci wurin.
Magajin garin na Chicago ya bayyana cewa, babbar manufarsa ta gayyata taron buda baki ita ce, kara dankon alaka a tsakanin mabiya addinai da ke birnin, domin kuwa a cewarsa musulmi wani bangare ne mai matukar muhimmanci a cikin jama'ar birninsa, saboda haka ya yi amfani da wannan damar ta watan ramadan domin hada musulmi da wadanda ba musulmi ba a wuri guda domin a kara samun dankon alaka da fahimtar juna.
Dangane da 'yan siyasar kasar da ma wasu mutanen gari da suke magangau na batunci da nuna kyama ga musulmi kuwa, magajin garin birnin na Chicago ya bayyan cewa suna tafka babban kuskure, domin kuwa Amurka kasa ce da ta hada mabiya addinai daban-daban, wanda ba zai yiwu ka kyamaci wani bangare ba saboda addininsa.
Salman Aftab wani daya daga cikin jagororin musulmi a birnin ya gabatar da jawabinsa na godiya dangane da karramawar da magajin garin birnin ya yi musu, ya kuma yi kira ga sauran 'yan siyasa da su koyi da irin wannan aiki, wanda zai kara kusanto da fahimtar juna atsakanin al'ummomin Amurka mabiya addinai daban-daban, maimakon tsangwamar musulmi da cin zarafinsu da ake yi a wasu bangarori na kasar.