Zanga-zangar Nuna Takaicin kashe Bakake A Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7801-zanga_zangar_nuna_takaicin_kashe_bakake_a_amurka
Daruruwan mutane ne suka yi maci zuwa dandalin TIME SQUARE dake birnin New York domin gudanar da zanga-zangar nuna kyamar su akan kashe wasu Amurkawa bakake biyu da suak hada da Philando Castile wanda aka kashe a Minesota da kuma wanda aka yi wa Alton Sterling a Baton Rauge dake Louisiana.
(last modified 2018-08-22T06:58:33+00:00 )
Jul 08, 2016 00:46 UTC
  • Zanga-zangar Nuna Takaicin kashe Bakake A Amurka

Daruruwan mutane ne suka yi maci zuwa dandalin TIME SQUARE dake birnin New York domin gudanar da zanga-zangar nuna kyamar su akan kashe wasu Amurkawa bakake biyu da suak hada da Philando Castile wanda aka kashe a Minesota da kuma wanda aka yi wa Alton Sterling a Baton Rauge dake Louisiana.

Masu zanga-zangar suna tafe suna daga hannuwan su suna cewa a daina harbi kuma suna kira da a yi adalci ga Bakaken Amurkawan da ‘yan sanda suka harbe.

 

Wannan kashe bakaken fatan har su biyu da aka yi cikin wannan satin ya tada wata alamar tambaya game da yadda ‘yan sanda ke anfani da karfi fiye da kima musammam akan tsiraru bakake.

 

Mafi akasarin masu zanga-zangar na cewa bakin ciki da rashin daukar matakin da ba ayi yasa su shiga cikin wannan zanga-zangar.

 

Yanzu haka dai ana zaman dar-dar a wasu birane na Amurka a sanadin harbin izgilanci da ‘yan sanda suka yi wa fararen hula, Bakaken Fatan biyu, mai cikeda ganganci.

 

An dai yi zanga-zanga ta farko a birnin Baton Rouge na jihar Louisiana inda jiya da dare dimbin mutane suka fito, suka tsaya a gaban wani dan shago inda a nan ne ‘yan sanda suka bindige bakin guda.

 

Wasu sun dauki kisan a kan wayoyinsu na hannu, abinda kuma aka warwatsa ko ina, abinda ya dada fusata mutane wadanda daman sun gaji da ganin yadda ake ta kara samun abkuwar irin wannan al’amarin na ‘yan sanda masu kashe mutane ta hanyar harbe su.

 

Wanda aka kashe a gaban wannan shagon a can Louisiana wani Bakar Fata ne mai suna Alton Sterling, 37, wanda akace ya tsaya gaban shagon ne, yana sayarda faya-fayinsa na CDs a lokacinda abin ya faru.

 

Yayinda ake juyayin wannan abinda ya faru a Louisiana ne sai gashi kuma irin hakan ta sake faruwa a jihar Minnesota inda wani dan sanda ya bindige wani Direba mai suna Philando Castile, 32, har lahira bayanda dan sandan ya tsaida motar mutumen a garin Falcon Heights.

 

Wanda aka kashe yana tareda wata mace da yaro jinjiri a cikin motar lokacinda dan sandar ya bindige shi.

 

kuma matar dake tare da mutimin ta dau hoton bidiyon yadda duk al'amarin ya auku, abunda ya kara fusata jama'a kan wannan aika-aika kawai akan bincike ababen hawa.

 

A halin da ake ciki dai a wani lamari da ake yi wa kallon daukan fasan, wasu da ba'a san ko suwa ne sun bude wuta kan 'yan sanda Amurka a Dallas a lokacinm irin wannan zanga-zanga inda suka harbi goma daga cikin su kuma hudu daga cikin su sun bakunci lahira, wasu kuma sunji munanen raunuka.

 

Shugaban kasar ta Amurka B. Obama ya kira wannan al'amari da yaki yaki cincewa da nuna banbanci musammam akan tsarin shari'ar kasar, wannan a cewarsa yafi shafar Amurkawa bakake da ‘yan Latino.

 

Wannan abin takaici na cin zarafi da kisan gilla da ba yau aka saba ganin irinsa ba a wannan kasa ta Amurka, duniya bata cika soma bakin ta ba a kai, balle ayi zancen yin allawadai.