Amurka: Kin Amincewa Da Muzgunawa Bakaken Fata
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7816-amurka_kin_amincewa_da_muzgunawa_bakaken_fata
Wata Sabuwar Zanga-zangar Allah Wadai da Kisan Bakaken Fata
(last modified 2018-08-22T06:58:33+00:00 )
Jul 08, 2016 14:27 UTC
  • Amurka: Kin Amincewa Da Muzgunawa Bakaken Fata

Wata Sabuwar Zanga-zangar Allah Wadai da Kisan Bakaken Fata

Babban magatakardar Majalisar Dinkin duniya, ya yi tir da kashe 'yan sanda a Amurka.

Ban Ki Moon wanda ya fitar da bayani a yau juma'a, ya yi tir da harbi da aka yi a birnin Dallas na Jahar Texas da ke Amurka wanda ya ci rayukan 'yansanda 5.

Wani kwararren maharbi ne da ya ja tunga a wani wuri, ya rika yi wa 'yan sandan dauki dai-dai,a yayin zanga-zangar da aka yi ta nuna rashin amincewa da kashe bakaken fata da jami'ar tsaro su ke yi.

A jiya alhami mai dai dubban mutanen kasar sun yi zanga-zangar yin tir da yadda ake kashe bakaken fata a cikin kasar.

A birnin Newyork dubban mutane sun yi zanga-zangar yin tir da yadda ake kashe bakaken fata, tare da yin kira da a hukunta 'yan sandan da su ke yin hakan.

Masu Zanga-zangar dai sun daga kwalaye da su ke dauke da take daban-daban da su ka hada da cewa; "Rayuwar bakaken fata tana da muhimmanci." sai kuma cewa; "Wajibi ne a kawo karshen amfani da karfin da 'yan sanda su ke yi."