Dan bn Ladan ya yi barazanar dauka fansa na kisan ma'aifinsa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7921-dan_bn_ladan_ya_yi_barazanar_dauka_fansa_na_kisan_ma'aifinsa
Dan bn ladan tsohon Shugaban Kungiyar Alka'ida ya yiwa Amurka barazanar cewa zai dauki bansar jinin Ma'aifinsa.
(last modified 2018-08-22T06:58:34+00:00 )
Jul 11, 2016 01:19 UTC
  • Dan bn Ladan ya yi barazanar dauka fansa na kisan ma'aifinsa

Dan bn ladan tsohon Shugaban Kungiyar Alka'ida ya yiwa Amurka barazanar cewa zai dauki bansar jinin Ma'aifinsa.

Tashar Telbijin din Rusiya Alyaum ta habarta cewa Hamza bn Ladan Dan tsohon shugaban Kungiyar 'yan ta'adda ta Alka'ida wato Usama bn Ladan cikin wani faifai sauti da ya watsa ta hanyar yanar gizo ya yiwa Amurka barazanar daukan fansa ta jinin ma'aifinsa.

A cikin sakon na dakikoki 21, Hamza bn Ladan ya yi barazanar cewa Kungiyar Alka'ida za ta ci gaba da yakar Amuka gami da kawayanta.

A shekarar 2011 ne Dakarun musaman na kasar Amurka suka hallaka Usama bn Ladan a maboyarsa dake kasar Pakistan.