An Sake Kashe 'Yan Sanda A Amurka
Rahotanni daga Amurka na cewa an harbe har lahira wasu 'yan sanda uku a Baton Rouge dake Louisiana, inda kwanan baya aka kashe wani matashi bakar fata.
kawo yanzu dai ba'a bayyana abunda ya hadasa musayar wutar ba, aman rahotannin sun ce an kashe daya daga cikin maharan uku yayin da biyu suka arce.
ko baya ga 'yan sanda da aka kashe akwai an ce akwai wasu 'yan sanda da dama da suka ji rauni sanadin harbin da aka yi masu, kamar yadda ita ma ma'aikatar 'yan sandan yanin ta tabbatar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin ake cikin zamen dar-dar a yankin na Louisiana inda aka shafe kwanaki ana zanga-zanga kyammar cin zarafi da kuma muzgunawa da 'yan sanda kasar keyi wa bakaken fata.
ko a kwanan baya ma dai an harbe har lahira 'yan sanda Amurka guda biyar a cikin irin wannan yanayi.