Musulmin Kashmir Na Neman Taimakon Kungiyar Kasashen Musulmi
Jagoran ‘yan aware yankin Kashmir na India ya aike da wata wasika zuwa kungiyar kasashen musulmi da wasu bangarori domin neman a dakatar da kisan jama’a a yankin.
Kamfanin dilalncin labaran Hamrain News ya bayar da rahoton cewa, jagoran ‘yan awaren yankin Kashmir na India Sayyid Ali Shah Gilani ya aike da wata wasika zuwa kungiyar kasashen musulmi da wasu bangarori na kasa da kasa domin neman a dakatar da kisan jama’a a yankin na Kashmir.
A cikin wasikar wadda ya aike zuwa ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen musulmi gami da shugaban kasar China, Gilani ya bukaci wadannan bangarori da su sa baki domin kawo karshen kisan da sojojin India suke yi wa musulmi.
Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce an kashe mutane kimanin 45 tare da jikkata wasu kimanin 3100 a hare-haren da ami’an sojin kasar India suke kaiwa kan musulmi na yankin Kishmir, sakamakon boren da suka tayar daga ranar Juma’ar makon da ya gabata.
Boren dai ya smo asali ne daga kisan gillar da jami’an tsaron India suka yi wa Burhan Muzaffar Wani, shugaban kungiyar Mujahidin Kishmir, wanda India ke kallonsa a matsayin dan ta’adda, an kasha shi ne a ranar Juma’ar makon da ya gabata bayan kamala sallar Juma’a tare da mukarrabasa biyu, daga nan kuma boren ya fara, bayan shudewar kwanaki goma har yanzu kura ba ta lafa ba.