Zanga-zangar Musulmi a Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i8563-zanga_zangar_musulmi_a_amurka
Dariruwan musulmi ne suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawarsu da masu gyamar musulmi da kuma aiyukan kungiyar ISIS a birnin Watsinton na kasar Amurka.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 24, 2016 06:51 UTC
  • Zanga-zangar Musulmi a Amurka

Dariruwan musulmi ne suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawarsu da masu gyamar musulmi da kuma aiyukan kungiyar ISIS a birnin Watsinton na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin Pars na kasar Iran ya habarta cewa A jiya Assabar dariruwan musulmi ne suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewar su da aiyukan masu gyamar musulinci gami da aiyukan 'yan ta'addar ISIS a birnin watsinton fadar milkin kasar Amurka.

Mahalarta zanga-zangar na rera taken rashin amincewar su da siyasar masu gyamar addinin musulincin a Amurka da kuma aiyukan ta'addanci na kungiyar ISIS, inda suka bayyana cewa  ta'addancin da kungiyar ISIS ke aikata ya yi hanun riga da koyarwar addinin islama.

A cikin makunin baya-bayan nan kungiyar ISIS din ta tsananta aiyukanta na ta'addanci a kasashen Amurka da Turai.