Kisan Mutane Akalla 4 A jihar Texas Na Kasar Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i8581-kisan_mutane_akalla_4_a_jihar_texas_na_kasar_amurka
An kashe Mutane 4 Sanadiyyar Harbi Da Bindiga A Jihar Texas Ta Kasar Amurka
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 24, 2016 09:43 UTC
  •  Kisan Mutane Akalla 4 A  jihar Texas Na Kasar Amurka

An kashe Mutane 4 Sanadiyyar Harbi Da Bindiga A Jihar Texas Ta Kasar Amurka

Majiyar jami'an tsaro a jihar Texas na kasar Amurka ta bayyana cewa wani dan bindiga dadi ya kashe akalla mutane 4 a wani rukunin gidaje a garin Bustroop na jihar a jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto kakakin yansanda a garin yana fadar cewa mutane hudu ne suka tabbatar da mutuwarsu a harbe harbe wanda da aka yi a jiya a garin Bustroop sannan wani yaro guda ya ji rauni.

Majiyar ta kara da cewa yansandan sun sami nasara kashe mutumin da ya yi kisan. Kakakin yansandan ya kara da cewa an kashe wanda ake zaton ya yi harbe harben ne bayan ya tsere zuwa wani wuri a jiya Asabar. A halin yanzu dai kome ya koma kamar yadda yake a garin..

Garin Bustroop dai yana da tazarar kilomita 56 daga birnin Texas, sannan yana da mutane kimani dubu 7. Dubban mutane ne suke mutuwa sanadiyyar harbi da bindiga a duk fadin Amurka a ko wace shekara.