Shugabar Jam'iyyar Democrat Ta Amurka Ta Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i8623-shugabar_jam'iyyar_democrat_ta_amurka_ta_yi_murabus
A Amurka, yayin da jam’iyyar demucrat za ta yi babban taron ta a yau Litinin domin tabbatar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton a matsayin ‘yar takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa, shugabar jam’iyyar Democrat ta kasar Debbie Wasserman Schultz tayi murabus.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 25, 2016 01:23 UTC
  • Shugabar Jam'iyyar Democrat Ta Amurka Ta Yi Murabus

A Amurka, yayin da jam’iyyar demucrat za ta yi babban taron ta a yau Litinin domin tabbatar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton a matsayin ‘yar takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa, shugabar jam’iyyar Democrat ta kasar Debbie Wasserman Schultz tayi murabus.

Schultz, ta bar aikinta biyo bayan kwarmata wasu sakonnin email dake nuna shugabar na wasu kalaman cin zarafi ga mai neman zama ‘dan takara Sanata Bernie Sanders, a lokacin da yake karawa da Hillary don neman zama ‘dan takara. 

Wasserman Schultz, wadda take ‘yar majalisa ce da ta fito daga jihar Florida, ana tsammanin za ta sauka daga mukaminta karshen makon nan bayan babban taron da za ayi a birnin Philadelphia.

Bernie Sanders dai ya bukaci Wasserman Schultz da tayi murabus, bayan da aka kwarmata bayanan da suka kunshi email akalla 2000, na shugabar jam’iyyar na tsawon akalla shekara ‘daya da rabi.