Harbi Kan Mai Uwa Da Wabi A Amurka Ya Dauki Rayuka
Jul 31, 2016 07:49 UTC
Wasu Mutane Sun mutu da kuma Jikkata A Harin Kan Mai Uwa Da Wabi A Garin Sten da ke jahar Texas Na Amurka
Majiyar bada agajin gaggawa a Texas ta ce a kalla mace guda ta rasa ranta, yayinda wasu uku su ka jikkata a harbin kai mai uwa da wabi a yankin Austin.
Majiyar ta ci gaba da cewa an yi harbin ne a yankin "Sixth Street" na shakatawa a tsakanin karfe 2 zuwa 3 na dare.
Jami'an tsaro sun yi kira ga mazauna yankin da su kaurewa fitowa waje, har zuwa lokacin da za a magance matsalar.
Amurka dai na fama da matsalar harbe-harbe da masu dauke da bindigogi su ke yi, wanda kuma a mafi yawancin lokuta ya ke haddasa asarar rayuka.
Tags