An Tsawaita Dokar Ta Baci A Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i901-an_tsawaita_dokar_ta_baci_a_faransa
"yan majalisa sun amunce da gagarimin rinjaye da kudirin
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 17, 2016 02:21 UTC
  • Dakarun kudun bala na Faransa
    Dakarun kudun bala na Faransa

"yan majalisa sun amunce da gagarimin rinjaye da kudirin

Majalisar dokokin Faransa ta amunce da gagarimin rinjaye da bukatar gwamnatin kasar na tsawaita dokar ta baci da watanni uku a duk fadin kasar.

'yan majalisu 212 ne suka amunce da kudirin, yayin da 31 suka ki amuncewa da hakan a jefa kuri'a da aka yi jiyya Talata.

Dama kafin hakan majalisar datijan kasar ta maunce da wannan kudirin da gagarimin rinjaye.

kasar Faransa dai na cikin shirin ko- ta- kwana tun a watan Nowamba bara, bayan da hare-haren ta'adancin da aka kai a Paris babban birnin kasar wanda suka yi sanadin mutuwar mutane 130 tare da jikkata wasu sama da 350.