Dariruwan Kananan Yara sun Mutu a Siriya sanadiyar Ta'addancin Saudiya
wakilin Siriya A MDD ya ce ta'addancin Saudiya yayi sanadiyar mutuwar kananan yara da dama a Siriya
A yayin da yake gabatar da Jawabi gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya dangane da yanayin kananan Yara a Siriya , Wakilin kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya ce daga cikin Rahoton da MDD ta bayar ba a gudanar da bincike kan irin kisan killa da kuma tozarta kananan yarar da aka yi a kasar Siriya sanadiyar mumunar akida ta kafirta Mutane da ta samo asali daga kasar Saudiya.
Ja'afari ya ce a kwai cibiya dake kula da aiyukan 'yan ta'adda a birnin Aman na kasar Jodan wacce aikinta tattare 'yan ta'adda daga kasashen Larabawa da sauren kasashe inda take tura su kasar Siriya a matsayin 'yan tawaye masu sassaucin ra'ayi, kuma wadanda 'yan ta'adda sun tabka ta'asa da ta'addanci ga kananan yara siriya.
Har ila yau Ja'afari ya kara da cewa Rahoton na MDD bai ambato irin tsananin wahala da Azaba da kananan Yaran Siriya ke fuskanta a yankin tudan Golan dake kalkashin mamayar haramcecciyar kasar Isla'ila ba, sannan kuma bai ambato dariruwan kananan yaran siriyan da 'yan ta'addar suka sace.
Har ila yau Wakilin Kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya ce ba za mu rufe idanunmu ba a kan ta'addancin da gamayyar wasu kasashen Larabawa kalkashin masarautar Ali sa'oud ke ci gaba da yi a kasar Yemen ba, da hakan ya yi sanadiyar shahadar dubun kananen yara na kasar Yemen din ba.