An bindige wani Dan sandar Amurka a jihar Georgia
Aug 15, 2016 02:01 UTC
Wani Dan bindiga ya hallaka wani Dan Sandar Amurka a jihar Georgia
Jami'an 'yan sandar Amurka sun sanar a wannan Lahadi cewa , wani Dan bindiga ya hallaka wani jami'in Dan Sanda guda a yayin da ya isa wata anguwa domin neman waya a kudanacin jihar Georgia
Jami'an 'yan sandar sun ce Dan sandar da aka kashe sunansa Tim Smith kuma yanada shekaru 31 a Duniya, tuni kuma aka fara gudanar da bincike domin gano wanda ya bindige shi,
Alkaluma sun ce cikin ko wata shekara Duban mutane ne suke rasa rayukansu ko kuma ake jikkata su a Amurkan ta hanyar bindigewa ko amfani da wani makami na daban kamar yuka da saurensu.
Tags