Kasashen Faransa Da Cuba Sun Cimma yarjejeniyoyin Da Dama
Bangarorin biyu sun cimma wadanan yarjejeniyoyin ne yayin ziyara da shugaban Raul Castro ya kai a Faransa.
Shugabanin kasashen Faransa da Cuba sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka shafi kasuwanci da hulda a tsakanin su.
Shugaban Francois Hollande da takwaran sa na Cuba Raul Castro sun cimma yarjejeniyoyin ne 12 a yayin ziyara da Castro ya kai a Faransa.
wannan ziyara dai na zamen mai cike da tarihi wace kuma zata bude alaka tsakanin kasashen biyu tun dai bayan cire takunkumi ga kasar ta Cuba.
A yayin taron manema labarai da bangarorin biyu suka yi a birnin Paris, shugaba Hollande domin taimakawa kasar Cuba farfado da tattalin arzikin ta, Faransa zata yafe wani bangaren bashin da take bin kasar ta Cuba.
Wanan dai ita ce ziyara Raul Castro ta farko a Turai tun lokacin da ya gaji yayansa Fidel Castro a 2006.