Fursunoni 61 Suka Rage A Gwantanamo
Aug 16, 2016 06:40 UTC
Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa fursunoni 61 suka rage a Gwantanamo, bayan data mika wasu 15 ga hadadiyyar daular Larabawa.
Sanarwar da ma'aikatar Pantagone ta fitar a wannan Litinin ta ce wannan shi ne adadin fursuna mafi yawa da aka fitar a Gwantanamo bisa umurnin shugaba Obama.
Tun a shekara 2009 ne Shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ke neman a rufe gidan kason na Gwantanamo da aka buda a lokacin gwamnatin tsohon shugaba G.W Bush bayan harin 11 ga watan Satumba domin tsare wadanda ake tuhuma da kitsa harin.
Shugaba Omaba dai ya sha alwashin rufe gidan yarin wanda ya ce bashi da wani amfani, hasali ma kara horar da 'yan ta'adda.
Tags