Amurka : Ci gaba Da Yin Suka Akan Halin Muguntar Jami'an Tsaro
An gudanar da zanga-zang a birnin Newyork na Amurka domin nuna kin amincewa da halin muguntar 'yan sandan kasar.
An gudanar da zanga-zang a birnin Newyork na Amurka domin nuna kin amincewa da halin muguntar 'yan sandan kasar.
Tashar Telbijin din Press tv ta nakalto cewa; Masu Zanga-zangar sun rika yin tir da halin 'yan sandan na kyamar bakaken fata da nuna musu halin mugunta.
Zanga-zangar dai an yi ta ne a karkashin kungiyar nan mai kare hakkokin bakaken fata da a ke kira ( Black Life Matters).
Bugu da kari, sun yi kira da a hukunta wadanda su ke da hanu wajen kashe bakaken fatar kasar.
A cikin watannin bayan nan dai kungiyar mai kare bakaken fata ta riga gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar ta Amurka domin nuna rashin dadinsu akan yadda ake kashe bakaken fata.