-
Firayi Ministan Italiya Yayi Murabus Bayan Shan Kaye A Zaben Raba Gardama
Dec 05, 2016 02:14Firayi ministan kasar Italiya Matteo Renzi ya yi murabus daga mukaminsa bayan mummunar kayen da ya sha a zaben raba gardamar da aka gudanar a kasar dangane da sauye-sauye da ake son yi a kundin tsarin mulkin kasar.
-
Hage Geingob: Namibiya Za Ta Ci Gaba Da Zama A Kotun ICC Matukar Amurka Ta Shigo
Dec 05, 2016 02:13Shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya sake jaddada aniyar kasarsa ta ficewa daga kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka ICC yana mai cewa kasar Namibiya za ta ci gaba da zama cikin yarjejeniyar Roma da ta kafa kotun ne kawai idan har Amurka ta shigo cikin kotun.
-
Wasu Daga Cikin Musulmin Birtaniya Na Dora Alhakin Harin 11 Ga Satumba A Kan Amurka
Dec 04, 2016 15:36Wani sakamakon jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Birtaniya ya nuna cewa kusan kashi daya bisauku na musulmin kasar na doran alhakin harin 11 ga satumba a kan Amurka.
-
Makarkashiyar Kungiyar Yahudawa A Kan Musulmi Dan Majalisa A Amurka
Dec 04, 2016 15:34Wani hamshakin mai kudi a kasar Amurka kuma daya daga cikin yahudawa masu kare manufofin Isra'ila a Amurka, ya tsaya kai da fata domin ganin an hana wani dan majalisar dattijan kasar musulmi rike shugabancin kwamitin zartarwa na jam'iyyar Democrat.
-
Rasha ta aika taimakon Ton 150 zuwa Birnin Halab na Siriya
Dec 04, 2016 07:41Rasha ta aika da taimako na Ton 150 zuwa yankunan da aka 'yanto na Birnin Halab a Kasar Siriya
-
Al'ummar kasar Cuba sun yi ban kwana da Fidel Castro
Dec 04, 2016 07:39Cikin wani yanayi na jimami da alhini shugaban kasar Cuba Raul Castro ya yi alkawarin ci gaba da akidar dan uwansa Fidel Castro.
-
Kasar China Ta Nuna Fushinta Da Tattaunawar Trump Da Shugabar Taiwan
Dec 03, 2016 14:34Kasar China ta bayyana tsananin fushinta dangane da tattaunawa ta wayar tarho da zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi kai tsaye da shugabar kasar Taiwan, da take kallon wajen a matsayin wani yanki na kasar China da ya balle.
-
Sojojin Siriya Sun Kwace Kashi 60% Na Garin Halab Daga Hannun 'Yan Ta'adda
Dec 03, 2016 14:34Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar sojojin kasar sun sami naasarar kwace sama da kashi 60% wato kusan kashi biyu cikin uku na yankunan gabashin birnin Halab (Aleppo) daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS) wadanda suke rike da shi na tsawon shekaru.
-
An bukaci Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan
Dec 03, 2016 07:51Majalisar Dinkin Duniya ta sake fitar da wani kudirin inda ya bukaci haramcecciyar kasar Isra'ila da ta fice daga tsaunukan Golan
-
Al'ummar kasar Faransa sun yi maraba da matakin Shugaba Holland
Dec 02, 2016 07:51Fiye da kashi 80% ne na Al'ummar kasar Faransa suka bayyana farin cikin su kan matakin da shugaba Holland ya dauka na rashin tsayawa takara a zaben 2017