Pars Today
Dubban mutanen kasar Aljeriya ne su ka gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da sake tsayawar takarar shugabanci na Abdulaziz Buteflika.
Kasar Uganda ta soki makwabciyarta Rwanda saboda rufe kan iyakar kasashen biyu.
A Najeriya adadin mutanen da cutar zazzabin lassa ta yi ajalinsu ya kai 83 a cewar hukumomin kiwna lafiya na kasar.
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da munanan hare-haren ta'addanci da aka kai Mogadishu, babban birnin Somalia.
Mambobin Kwamitin zaman lafiya sun shiga ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya Aso Rock.
Tsohon Firai Ministan kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar Hadaddiyar daular larabawa tana da hannu a kokarin gurgunta demokradiyar kasar Tunisiya.
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu tana goyon bayan mutanen kasar Venezuela don fayyace makomar kasarsu.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Senegal ta fitar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, tda ke tabbatar da cewa Macky Sall ne ya sake lashe zaben.
Mambobin kwamitin tababtar da zaman lafiya kan sha’anin zaben Najeriya karkashin shugabancin tsohon shugaban mulkin soji a najeriya Abdussalami Abubakar sun gana dad an takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Mutane akalla 20 aka tabbatar da mutuwarsu da kuma wasu 43 da suka ji rauni sanadiyar hatsarin jirgin kasa da kuma gobarar da ta biyo baya a wata tashar jiragen kasa a birnin Alkahira na kasar Masar a jiya Laraba.