Najeriya : Adadin Wadanda Zazzabin Lassa Ya Kashe Ya Kai 83
A Najeriya adadin mutanen da cutar zazzabin lassa ta yi ajalinsu ya kai 83 a cewar hukumomin kiwna lafiya na kasar.
Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Nijeriya, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin lassa a fadin kasar ya kai 83.
A cikin sanarwa data fitar cibiyar ta NCDC ta fitar, ta ce adadin ya dauki kaso 21.8 na wadanda suka mutu sanadiyyar cutar, tun bayan barkewarta a cikin watan Junairu.
Kuma a cewar sanarwar Jihohi a kalla 21 ne daga cikin 36 suka fuskanci barkewar cutar mai sanya matsanancin zazzabin.
An kuma samu sabbin wadanda suka kamu da cutar ne tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga watan Fabreru da ya shude.
A cewar cibiyar, kawo yanzu, mutane 1,279 ne ake zargin sun kamu da cutar a fadin kasar.