Nijar / Olympics Rio : Isufu Ya Jinjinawa Abdulrazak Alfaga
Shugaban kasar Nijar Alhaji Mahamadu Isufu tun daga kauyensa na Dan Daji dake jihar Tawa inda yake hutu, ya jinjinawa Abdulrazak Isufu Alfaga dan wasan kokawar Taekwondo kan ciyo wa kasar lambar yabo ta Azurfa a gasar wassanin Olympics.
Wannan dai shi ne karon farko da jamhuriyar Niger ta samu lambar yabo tun bayan tagulla da dan kasar, Issaka Daborg ya samu a gasar dambe a Munich a 1972.
Hakan dai ya sa Nijar ta kasance cikin jerin kasashen Afrika da suka haska a wasannin da aka kammala jiya Lahadi, inda har ma ta dara makofciyyarta Najeriya data samu lambar yabo ta tagulla a kwallon kafa na maza 'yan kasa da shekaru 23.
A jiyya ne dai aka rufe wassanin na Olympics 2016 da birnin Rio de Janairo na Brazil ya dauki bakunci.
Amurka ce dai ta sake lashe yawan lambobin yabo ko a wannan karo da lambobi 121 mafi yawa na zinari, sai Biritaniya mai 67 sai kuma kasar Sin mai lambobi 70 aman a mataki daban daban.
A nahiyar Afrika dai Afrika ta kudu ce sahun gaba, sannan akwai kasashen kenya, Cote d''ivoire, Habasha, Burundi,Aljeriya, Masar, Tunusiya da suma suka haska a wassanin.
Yanzu dai birnin Rio de Janairo na Brazil ya mikawa birnin Tokiyo na Japon ragamar shirya wassanin na shekara 2020 idan Allah ya kai.