An BUde Taron Farko Na Kusanci A Tsakanin Mazhabobin Musulunci A Masar
Aug 26, 2016 07:16 UTC
Taron hadin kan mazahabobi a masar
An budetaron farko na hadin a tsakanin mazhabobin musulunci a kasar Masar.
Wani Malamin Jami'ar Azhar wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron, Ahmad Karimah yayi ishara da rawar da Azhr ta taka wajen hada kan mazhabobin musulunci da kusanto da fahimtar juna, sannan ya kara da cewa; Mazhabobin Shi'a da Sunna basu kafrita junansu, kuma jami'ar Azhar ta yarda da yawaitar mazhabobi.
Malamin ya ci gaba da cewa kawo ya zuwa yanzu malaman mazhabar shia a Iraki da Iran sun fitar da fatawowi 22 da haramta cin zarafin duk wani abu da ahlussunah su ke girmamawa.
Tags